Kwallon kafa

FIFA ta shafe makin da Sudan ta ci Zambia

Tambarin hukumar FIFA
Tambarin hukumar FIFA Reuters

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, wato FIFA, ta shafe makin da kasar Sudan ta samu a wasanta da ta buga da kasar Zambia inda ta lallasa ta da ci 2-0, a wasan fidda wadanda su ka cancanta su halarci gasar cin kofin duniya.

Talla

FIFA dai ta shafe makin da kasar ta Sudan ta samu ne bayan an gano cewa daya daga cikin ‘Yan wasanta bai cancanta ya buga wasan ba, domin ya na da yellon katuna, wato yellow cards daya samu a wasannin da aka buga a baya.

Har ila yau an ci taran hukumar kwallon kafar kasar Sudan kudi Dalar Amurka dubu shida da dari hudu da talatin, baya ga mika maki uku da aka wa kasar Zambia.

A yanzu haka Zambia ce ke kan gaba a rukunin na su na na rukunin “D” a yayin da ita Sudan din ta koma jeri na uku a rukunin. Ghana ce dai ta biyu a yanzu haka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI