Kwallon Kafa

Faransa da Sweden sun sha da kyar, Spain ta yi kuka da Fabregas

Dan wasan Spain Cesc Fabregas a lokacin da ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida
Dan wasan Spain Cesc Fabregas a lokacin da ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida REUTERS/Juan Medina

A wasannin neman shiga gasar cin kofin Duniya da aka gudanar, Spain mai rike da kofin gasar ta yi kunnen doki ne ci 1-1 da Faransa. An shiga mintinan karshe a kammala wasa ne Olivier Giroud ya barke kwallon da Spain ta zira a ragar Faransa. Sau ra kadan Spain ta lashe wasan sadoba Fabregas ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Talla

Wasa tsakanin Jamus da Sweden kuma an tashi ne ci 4-4. Jamus dai ba ta sha da dadi ba domin sai da ta zira kwallaye Hudu a ragar Sweden kafin daga bisani Sweden ta barke kwallayen.

Wasa tsakanin Portugal da Ireland ta arewa an tashi ne ci 1-1. A wasan ne kuma Cristiano Ronaldo ya haska sau 100 a tawagar Portugal.

Wasan Ingila da Poland kuma an dage wasan ne zuwa yau Laraba saboda ruwan sama da aka tabka a birnin Wawsaw.

A yakin Amurka kuma da Caribbean, kasar Amurka ta lallasa Guatemala ci 3-1. Kuma Clint Dempsey dan wasan Tottenham shi ne ya zira wa Amurka kwallaye biyu a raga.

Kasar Jamaica kuma ta doke Antigua ne ci 4-1.

Canada kuma tasha kashi ne ci 8-1 hannun Hunduras. Amma Panama ta yi kunnen doki ne ci 1-1 da Cuba. Costa Rica kuma ta lallasa Guyana ne ci 7-1

Kasashe uku ne de ake bukatar su tsallake zuwa Brazil daga yankin Amurka da Carribiean.

A yankin Asiya kuma Australia ta doke Iraqi ci 2-1, kamar yadda Oman ta doke Jordan ci 2-1. A rukunin B dai kasar Japan ce ke jagorancin Rukunin da maki 10. Amma a wasan sada zumunci Japan din ta sha kashi hannun Brazil ci 4-0 a jiya Talata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.