Kwallon kafa

Senegal na neman sassauci daga hukumar CAF

A lokacin da Seneagl da Cote d'Ivoir ke karawa a Dakar
A lokacin da Seneagl da Cote d'Ivoir ke karawa a Dakar Reuters/Mamadou Gomis

Hukumar kwallon kafara kasar Senegal ta roki, hukumar kwallon kafar Nahiyar Afrika ta CAF da kada ta kara mata wani hukunci bayan wanda ta kakaba mata, wanda ya haramta mata zuwa gasar cin kofin nahiyar. A jiya dai hukumar ta CAF, ta bayyana cewa ta haramtawa kasar ta Senegal halartar gasar bayan ‘Yan kallon wasa sun jefa kwalabe da duwatsu a cikin filin wasa a lokcain da kasar ta ke karawa da Cote d’Ivoir a ranar Asabar, wanda hakan ya tilasata tsayar da wasan.  

Talla

Baya ga haka, Hukumar ta CAF, har ila yau a jiyan ta ce akwai wani hukunci kuma da zai biyo bayan haramtawa kasar ta Senegal zuwa gasar.

Amma a wata ganawa da shugaban hukumar kwallon kafar kasar ta Senegal, Augustine Senghor, sun amince da hukunci na CAF, amma suna rokon da kada a kara masu wani hukunci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI