Kwallon Kafa

Ingila ta yi kunnen doki da Poland

Rooney da Gerrard suna tabewa bayan Rooney ya zira kwallo a ragar Poland
Rooney da Gerrard suna tabewa bayan Rooney ya zira kwallo a ragar Poland REUTERS/Darren Staples

Wasa tsakanin Ingila da Poland an tashi ne kunnen doki ci 1-1, bayan dage wasan a ranar Talata zuwa jiya Laraba saboda ruwan sama a birnin Wawsaw. Wayne Ronney ne ya fara zirawa Ingila kwallo a ragar Poland, kwallon shi ta 30 da ya zira wa Ingila a raga.

Talla

Ana minti 70 da wasa ne kuma Kamil Glik ya barke kwallon a ragar Ingila.
Sai dai Ingila ce ke jagorancin Teburin rukuninsu na H, maki daya tsakaninta da Montenegro.

Steven Gerrard da Rooney sun amsa cewa sun buga wasan jiya ba kamar yadda suka saba ba. Amma ‘yan wasan sun ce sun yi imanin Ingila za ta tsallake zuwa gasar cin kofin Duniya a Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.