Tseren Keke

An karbe wa Armstrong nasarorin da ya samu a Tour de France

Lance Armstrong tsohon zakaran  gasar Tour de France 2002.
Lance Armstrong tsohon zakaran gasar Tour de France 2002. REUTERS/Eric Gaillard/Files

Hukumar tseren keke ta duniya ta karbe kambunan da Lance Armstrong ya lashe guda bakwai a gasar Tour de France tare da dakatar da shi shiga duniyar wasannin Tsereb keke bayan kama shi da laifin kwankwadar kwayu da ke sa kuzari.

Talla

Yanzu haka kuma wani Kamfanin Inshora ya bukaci Armstrong ya biya wasu kudaden lada da ya karba kusan sama da Dala Miliyan Bakwai bayan ya lashe kofin Tour de France na shida a shekarar 2004.

Shugaban Kamfanin na Inshora yace za su shigar da kara idan har babu alamun Arsmtrong zai biya kudaden nan da kwanaki biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI