Kwallon kafa

PSG na burin Ibrahimovic ya maimaita bajintarsa akan Rennes

Zlatan Ibrahimovic
Zlatan Ibrahimovic REUTERS/Benoit Tessier

Club din Paris Saint Germain dake kasar Faransa na saka ido akan dan wasanta, Zlatan Ibrahimovic, inda suke sa ran zai maimaita irin bajintar da ya nuna a wasan sada zumunci da kasarsa ta Sweden ta buga da kasar Ingila inda ya zira kwallaye hudu shi kadai.

Talla

A gobe Asabar ne dai PSG zata kara da club din Rennes a gasar French Ligue, inda a karshen satin da ya gabata ne PSG ta yayi kunnen doki da club din da Monteplier wacce ita ke rike da kofin gasar.

A shekaran jiya ne kasar Sweden ta lallasa kasar Ingila da ci 4-1 a wasannin da aka buga na sada zumunci a wurare daban-daban a duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.