Wasan Dambe

An nemi Pacquiao ya yi ritaya daga fagen dambe

Dan wasan Damben kasar Philippine, Manny Pacquiao
Dan wasan Damben kasar Philippine, Manny Pacquiao mages.lpcdn.ca

A yanzu haka anata kira ga dan wasan damben kasar Philippine, Manny Pacquiao, da ya yi ritaya bayan shan kayin da yayi a hanun, Juan Manuel Marquez, dan kasar Mexico a ranar Asabar din da ta gabata a birnin Las Vegas dake kasar Amurka.

Talla

Dan wasan damben kasar Birtaniyan nan Ricky Hatton, ne ya fara yin kira ga Pacquiao ya yi murabaus inda ya ce, babu abin da ya rasa a fagen wasan dambe.

Pacquiao dai sau takwas yana lashe kambun zakaran duniya a fagen wasan na dambe.

Rahotanni na nuna cewa, matarsa wacce ake kira Jinkee tare da mahaifiyarsa, wato Dionisia suma sun nemi daya jingine safar dambensa.

Pacquiao, wanda zai cika shekaru 34 sati mai zuwa, sau hudu shime dai yana doke Marquez.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.