Kwallon kafa

Anelka zai fice daga Shenghai Shenhua

Nicolas Anelka
Nicolas Anelka

Tsohon dan wasan club din Chelsea, Nicolas Anelka, wanda a yanzu ke bugawa club din Shenghai Shenhua dke kasar China, wato Sin, ya fara tattaunawa da hukumomin club din domin kawo karshen zamansa a club din.

Talla

Rahotanni na nuna cewa, Anelka wanda ya taba bugawa Arsenal, Real Madrid, Manchsetre City da Bolton har ila yau da Chelsea, zai koma buga wasa a fagen wasan Premiere League, inda ake alakanta dan wasan da komawa Queen’s Park Rangers.

A dai farkon kakar wasan da ta gabata ne Anelka ya koma Shenghai Shenhua.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.