Kwallon Kafa

Cristiano ya ce ba zai tsawaita kwantaragin da ke tsakaninsa da Real Madrid ba

A wani labarin da jaridar kasar Spain mai suna AS ta buga a yau din nan na cewa shahararren dan wasar kwallon kafar nan da ke bugawa Real Madrid wato Cristiano Ronaldo ya ce ba zai tsawaita kwantaragin da ke tsakaninsa da Real Madrid inda har wannan kwantaragi ya kawo karshe a ranar 30 ga watan Yunin shekara ta 2015 idan Allah ya kai mu ba.

Talla

Jaridar ta jiyo dan wasar yana cewa, duk da yiyuwar kara masa wasu makuddan kudade domin ya ci gaba da bugawa kungiyar har zuwa shekarar 2018, wanda haka zai ba shi damar samun Euro milyan 15 bayan an cire kudin haraji wato karin 50% kenan akan abin da Real Madrid ke ba shi a halin yanzu, to amma ba zai tsawa a cikin wannan team ba.

Kuma tuni masana harkokin wasar kwallon kafa suka yi hasashen cewa Ronaldo yana shirin koma Paris Saint-Germains bayan karewar yarjejeniyar da ke tsakaninsa da Real Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.