Wasanni

Beckam ya ce ba zai yi gaggawar zaben kulob ba

Dan wasan kasar Ingila David Beckham.
Dan wasan kasar Ingila David Beckham. REUTERS/Brandon Malone

Tsohon dan wasan kungiyar Manchester United, David Beckham ya ce ba zai yi saurin daukar wani mataki ba, yayin zaben kungiyar da zai buga wa wasa, daga kungiyoyin da suke mishi tayi daga sassan duniya da dama. Beckham ya bar kungiyar LA Galaxy ta Califonia, a farkon wannan watan, bayan da ya taimaka mata, ta sami nasara a gasar MLS cup, yanzu kuma yana neman kulob din da watakil a ciki, zai karasa rayuwar shi ta wasan kwallon kafa.