Wasanni

Drogba zai jagoranci 'yan wasa Cote D'Ivoire

Didier Drogba na kasar Cote D'Ivoire
Didier Drogba na kasar Cote D'Ivoire Reuters

Shahararren dan wasan kasar Cote D’Ivoire Didier Drogba ne zai jagoranci ‘yan wasan kasar shi, yayin gasar cin kofin nahiyar Afrika da za a fara a ranar 19 ga watan Junairu mai zuwa. Jerin sunayen ‘yan wasan kasar da aka fitar, ya nuna cewa dan wasan, da yanzu haka ke buga wasannin kulob a kasar China, zai zama kyaftin din tawaggar kasar, mai ‘yan wasa 23.Drogba zai dauki wannan nauyin ne, bayan da ‘yan kasar suka gagara daukar kofin, a shekarar 2012, sakamakon nasarar da kasar Zambiya ta samu a kansu, a bugun daga kai sai mai tsaron gida, a wasan karshe na wancan lokacin.