Spain-Italiya

Cristiano ya zira kwallaye Uku a raga, Juve ta doke Milan

'Yan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo tare da Angel di Maria
'Yan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo tare da Angel di Maria REUTERS/Sergio Carmona

Cristiano Ronaldo ya fara hucewa da Celta Vigo domin ya zira kwallaye uku a raga da ya ba Real Madrid nasara ci 4-0 a gasar Copa del Ray zagayen Quarter Final. Kungiyar Juventus ta doke AC Milan ci 2-1 a zagayen Qauter Final a gasar cin kofin kalubalen Italiya.

Talla

A karawar Farko dai Celta Vigo ce ta doke Real Madrid ci 2-1.

Ronaldo wanda Messi ya doke a zaben gwarzon dan wasan Duniya, ya fara bude raga ne ana minti biyu da fara wasa.

A yau Alhamis ne kuma Barcelona za ta kara da Cordoba.

A Italiya kuma Juventus da ke jagorancin Teburin Seria A ta doke AC Milan ci 2-1.

Minti shida da fara wasa ne dan wasan Milan Stephan El Shaarawy ya fara zira kwallo a raga kafin daga bisani Sebastian Giovinco ya barke wa Juve kwallon. Ana kuma mintinan karshe ne Juventus ta sake jefa kwallo ta biyu a ragar Milan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.