Kwallon kafa

Yau Faransa za ta kara da Jamus, Ingila da Brazil a wasannin sada zumunci

'Yan wasan kasar Faransa
'Yan wasan kasar Faransa femmenligne.files.wordpress.com

A wasannin sada zumunci da za a yi a yau Laraba, kasar Faransa zata fafata da kasar Jamus, a yayin da ‘Yan wasan Ingila zasu kara da Brazil. Sauran wasannin da za buga sun hada da tsakanin Chile da Masar, Turkiya da Czech a dai dai lokacin da Sweden zata kara Argentina.  

Talla

Wadannan wasannin na zuwa a dai dai lokacin da za a cigaba da wasannin share fagen shiga gasar Cin Kofin Duniya a Brazil a shekara mai zuwa.

A jiya Talata, kasar Senegal da Guinea sun ta shi a kunnen doki da ci 1-1 a yayin da Armenia da Luxenbourg suma suka tashi da ci 1-1.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.