Kwallon kafa

Ban ji dadin doke Manchester United ba, inji Ronaldo

Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo
Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya cewa bai ji dadi ba da Real Madrid ta lallasa kungiyar Manchester United, wanda hakan ya fitar da ita Manchester daga gasar Zakarun Nahiyar Turai a zagayen kusa da na karshe, wato Quarter Finals. 

Talla

Ronaldo dai shi ya zira daya daga cikin kwallayen wasan a minti na 69 wanda hakan ya bawa Real Madrid samun nasarar lashe wasan da ci 2-1, ko kuma da ci 3-2 idan aka yi jumallar kwallayen da aka yi a wasannin biyu.

Rahotanni sun nuna cewa, a lokacin da Ronaldo ya shiga filin da za a fara wasan, ya samu tarba sosai daga ‘yan kallon, wanda wasu ke ganin hakan ya sa ya ki nuna farin cikinsa bayan ya zira kwallo a ragar Manchester United inda a nan ya kwashe kakar wasannin shida a kamin ya koma Real Madrid.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.