Champions League

Manchester da Donetsk sun fice, Madrid da Dortmund sun tsallake

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson yana nuna bacin ran shi bayan alkalin wasa ya ba Nani Jan kati a wasan da suke karawa da Real Madrid a Old Trafford
Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson yana nuna bacin ran shi bayan alkalin wasa ya ba Nani Jan kati a wasan da suke karawa da Real Madrid a Old Trafford REUTERS/Phil Noble

Real Madrid ta fitar da Manchester United a gasar zakarun Turai da jimillar kwallaye ci 2-3, bayan an tashi wasa a Old Trafford ci 1-2, a Santiago kunnen doki ci 1-1. Nani na Manchester United ya karbi jan kati a wasan.

Talla

Bayan dawowa hutun rabin lokaci a wasan, an kwashe tsawon minti 35 Manchester United na wasa da ‘Yan wasa 10 bayan alkalin wasa ya sallami Nani da Jan kati.

Bayan kammala wasan Sir Alex Farguson kocin Manchester ya kauracewa manema labarai saboda fusata da alkalancin wasan amma mataimakinsa Mike Phelan yace Alkalin wasa ne ya ya cuce su.

“Alkalin wasa ne ya bata wasan bayan ya salami Nani daga fili, na tabbata duniya sun ga me ya faru kuma sun ga yadda Manchester ta taka kwallo”. A cewar Phelan.

Mourinho kocin Real Madrid ya jajantawa ‘Yan wasan Manchester United tare da yabawa da yadda ‘yan wasan suka taka kwallo.

“Manchester United sun taka kwallo tare da hada kansu kuma sun yi iya kokarinsu. Modric ne ya canza salon wasan amma na tabbata ba don an rage yawan ‘yan wasan Manchester ba da ba za mu iya lashe wasan ba”. Inji Mourinho

Mourinho yace hakan ya taba faruwa da shi lokacin da alkalin wasa ya sallami dan wasan shi Pepe a wasan kusa da karshe da ya sha kashi hannun Barcelona.

A daya bangaren kuma, Borussia Dortmund ma ta tsallake zuwa zagayen kwata Fainal a karon farko cikin shekaru 15 bayan ta lallasa Shakhtar Donetsk a gida ci 3-0.

A karawar farko dai kungiyoyin biyu sun tashi wasa ne ci 2-2 wanda ya ba Dortmund jimillar kwallaye 5-2.

Wannan ne karon farko tun shekarar 1998 rabon Dortmund ta tsallaka zuwa zagayen kwata Fainal.

A yau ne kuma juventus za ta karbi bakuncin Celtic bayan Juve ta lallasa ta ci 3-0 a karawar farko.

Valencia kuma za ta kai wa PSG ziyara ne amma a karawar farko PSG ke da nasara da ci 2-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.