Champions League

PSG da Juventus sun fitar da Valencia da Celtic

Zlatan Ibrahimović Dan wasan PSG
Zlatan Ibrahimović Dan wasan PSG Reuters

A karon farko bayan shekaru 18 kungiyar PSG ta tsallake zuwa zagayen kwata Fainal, kamar yadda Juventus ta tsallake a karon farko cikin shekaru bakwai bayan kungiyoyin biyu sun fitar da Valencia da Celtic.

Talla

PSG ta tsallake ne da jimillar kwallaye ci 3-2 bayan ta doke Valencia 2-0 a Faransa sannan a daren jiya suka yi kunnen doki ci 1-1 a Spain.

Juventus da ta lashe kofin gasar Zakarun Turai a 1985 da 1996, a bana ta tsallake zuwa kwata Fainal ne da jimillar kwallaye ci 5-0 bayan doke Celtic gida da waje.

A daya bangaren kuma kocin Manchester United da Sir Alex Ferguson da shi da ‘yan wasan kungiyar za su fuskanci fushin hukumar EUFA bayan sun kauracewa manema labarai saboda zargin alkalin wasa ya cuce su a wasansu da Real Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.