Champions League

Barcelona ta lallasa AC Milan, Galatasaray ta yi waje da Schalke 04

Lionel Messi na Barcelona yana murnar zira kwallo a ragar AC Milan
Lionel Messi na Barcelona yana murnar zira kwallo a ragar AC Milan REUTERS/Albert Gea

Kungiyar Barcelona ta tsallake zuwa zagayen Kwata Fainal bayan lallasa AC Milan ci 4-0. Kum Barcelona ta ba marada kunya ne domin ta rama kashin da ta sha ne a gidan Milan ci 2-0. Galatasaray ta yi waje da Schalke 04 da jimillar kwallaye ci 4-3 bayan ta bi Schalke har gida ta doke ta ci 3-2.

Talla

Tun kafin zuwa hutun rabin lokaci ne Messi ya rama kwallaye biyu da AC Milan ta zira a ragar Barcelona a karawa ta farko. Inda ana minti biyar da fara wasa ne Messi ya jefa kwallo ta farko, ana saura minti Biyar aje hutun rabin lokaci ya sake jefa kwallo ta biyu.

David Villa da Jordi Alba su ne ‘yan wasan da suka zira sauran kwallayen a ragar AC Milan.

Yanzu haka Messi yana da jimillar kwallaye 58 a gasar zakarun Turai inda ya sha gaban Ruud van Nistelrooy da tazarar kwallaye biyu.

Messi yanzu yana neman kamo kafar Raul Gonzalez wanda ya jefa kwallaye 71 a raga.

Mataimakin kocin Barcelona Jordi Raura, yace Messi ya nuna shi zakaran duniya.
Kocin AC Milan Milan kuma ya amsa shan kashi yana mai cewa Barcelona kungiyar ce da babu irinta a duniya.

Wannan ne dai karo na Uku da Barcelona ke yin waje da AC Milan a kaka 8 da ake gudanar da gasar zakarun Turai

A daya bangaren kuma, Galatasaray ta yi waje da Schalke 04 da jimillar kwallaye ci 4-3 bayan ta bi Schalke har gida a daren jiya ta doke ta ci 3-2.

Wannan ne karon farko da Galatasaray ta tsalllake zuwa zagayen kwata Fainal tun a shekarar 2001

Yanzu dai Barcelona da Galatasaray sun bi sahun Real Madrid da Borussia Dortmund da Juventus da Paris Saint-Germain wadanda tuni suka tsallake zuwa kwata Fainal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.