Europa League

Chelsea da Tottenham da Newcastle sun sha da kyar

'Yan wasan kungyar chelsea
'Yan wasan kungyar chelsea

Chelsea da Tottenham da Newcastle sun tsallake zuwa zagayen kwata fainal a gasar Europa league bayan sun sha da kyar a daren jiya. Hakan ke nuna kungiyoyin Ingila sun mayar da martani a Europa league, bayan ficewar Manchester United da Arsenal a gasar zakarun Turai.

Talla

Tottenham ta sha da kyar ne saboda ta sha kashi ci 4-1 a hannun Inter Milan a daren jiya. Amma ta tsallake ne saboda kwallo daya da Adebayor ya zira a raga bayan lallasa Inter ci 3-0 a karawa ta farko.

Fernando Torres ne kuma ya taimakawa Chelsea zira kwallo ta uku a ragar Steaua Bucharest wanda ya ba Chelsea nasara a Stamford Bridege.

A daya bangaren kuma Papis Cisse shi ne ya zirawa Newcastle kwallo a ragar Anzhi Makhachkala bayan kungiyoyin biyu sun tashi babu ci a karawa ta farko.

Hakan ke nuna kungiyoyin Ingila sun mayar da martani a Europa league, bayan ficewar Manchester United da Arsenal a gasar zakarun Turai.

A daya bangaren kuma Benfica ta fitar Bordeaux da jimillar kwallaye ci 4-2, kamar yadda Lavente ta sha kashi a hannun Rubin kazan ci 2-0.

Kungiyar Basel ta Switzerland ta tsallake ne zuwa zagayen kwata Fainal duk da ta sha kashi ci 1-0 a hannun Zenit St Petersburg ta Rasha.

Fenerbahce ta Turkiya ta tsallake da jimillar kwallaye ci 2-1 bayan ta yi kunnen doki da Viktoria Plzen ta Jamhuriyyar Czech

Lazio ta doke Stuttgart ci 3-1, Wanda ya ba kungiyar nasarar tsallakewa zagayen kwata Fainal da jimillar kwallaye ci 5-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.