Champions League

An hada Barca da PSG, Bayern da Juve, Madrid da Gala, Malaga da Dortmund

Tambarin gasar Zakarun Turai
Tambarin gasar Zakarun Turai

A gasar Zakarun Turai an hada FC Barcelona wasa da Paris Saint-Germain da ke tashen kudi a Faransa a zagayen Kwata Fainal bayan an hada kungiyoyin da za su kara da juna a birnin Nyon na kasar Switzerland.

Talla

Bayern Munich da ta buga wasan karshe a bara, an hada ta wasa ne da Juventus.

Real Madrid da ke neman lashe kofin gasar karo na 10 an hada ta wasa ne da Galatasaray da ke naman zama kungiya ta farko daga Turkiya da za ta lashe kofin gasar a bana.

An hada kugiyar Malaga wasa da Borussia Dortmund da ta buga wasan karshe a 1997.

Za’a fara karawar farko a ranakun 2 da 3 na watan Afrilu, sai karawa ta biyu a ranakun 9 da 10.

A ranar 25 ga watan Mayu ne za’a gudanar da wasan karshe a filin wasa na Wembley a Birtaniya.

A karon farko, a bana za’a gudanar da wasanni Kwata Fainal ba tare da kungiyoyin Ingila ba tun a shekarar 1996.

A tarihin gasar, wannan ne karon Farko da aka samu kungiyar da ke rike da kofin gasar ta fice bayan ficewar Chelsea tun a zagayen farko.
 

Paris Saint-Germain (Faransa) da Barcelona (Spain)

Malaga (Spain) da Borussia Dortmund (Jamus)

Real Madrid (Spain) da Galatasary (Turkiya)

Bayern Munich (Jamus) da Juventus (Italiya)
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.