Kwallon Kafa

An haifawa Cassano Namiji kuma ya rada masa sunan Messi

Antonio Cassano Dan wasan Inter Milan
Antonio Cassano Dan wasan Inter Milan REUTERS/Giorgio Perottino

A ranar Litinin ne Matar Antonio Cassano mai suna Caroline ta Haifa wa dan wasan jariri nimiji. Kuma Dan wasan na Intar Milan ya radawa Jaririn sunan Messi kamar yadda ya sanar.

Talla

Cassano yace ya radawa Dan sa sunan messi ne saboda babu dan wasa irinsa a duniya.

Wasu dai suna ganin Cassano ya rada wa yaronsa sunan Messi ne saboda kwallaye biyu da ya barkewa Barcelona a ragar AC Milan a gasar zakarun Turai.

Cassano tsohon dan wasan AC Milan ne kafin daga baya ya koma taka kwallo a Inter Milan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.