Tseren Keke

Armstrong ya karyata rahoton zai canza sheka zuwa wasan iyon ruwa

Dan tseren gudun keke Lance Armstrong agasar Tour de France
Dan tseren gudun keke Lance Armstrong agasar Tour de France REUTERS/Philippe Wojazer

Dan tseren gudun Keke Lance Armstrong ya musanta rahoton zai shiga gasar tseren iyon ruwa da za’a gudanar a birnin Texas bayan samun haske daga hukumar wasannin.

Talla

Tun da farko ne dai aka ruwaito dan tseren keke Lance Armstrong wanda ya amsa yana kwankadar kwayu ya fara shirin canza sheka zuwa gasar tseren iyon ruwa, inda aka ce a karshen makon nan Armstrong yana cikin ‘yan wasan da za su haska a gasar iyon ruwa ta Masters da za’a gudanar a Texas.

Armstrong kuma zai shiga gasar iyo ne domin ba ta karkashin hukumar yaki da kwankwadar kwayu ta Amurka.

A watan Agusta ne aka haramta wa Armstrong kofunan da ya lashe a gasar Tour de france, inda kuma ya fito ya amsa yana kwankwadar kwayu a lokacin da ya ke zantawa da Oprah Winfrey a shirinta na Telebijin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI