Arsenal ba ta cire rai ba a gasar Zakarun Turai a badi, inji Wenger

Arsène Wenger, Kocin kungiyar Arsenal
Arsène Wenger, Kocin kungiyar Arsenal REUTERS/Phil Noble

Kocin Arsenal Arsene Wenger yace yana da kwarin giwar za’a kammala Premier suna cikin jerin kungiyoyi hudu a saman Teburin gasar duk da a daren jiya Talata Arsenal ta yi hasarar maki 2 bayan an tashi wasa babu ci tsakaninta da Everton. Yanzu kuma tazarar maki 2 ne Arsenal ta ba Chelsea da Tottenham amma dukkaninsu suna da kwanten wasanni.