Tennis

An kara kudi a Rolland Garros, Nadal yana neman lashe kofin Monte Carlo karo na 9

Rafael Nadal
Rafael Nadal

An samu karin kudi a gasar French Open a bana zuwa euro Miliyan 22. Duk wadanda suka lashe gasar a bangaren maza da mata a bana zasu kwashi kudi Euro Miliyan 1.5 kusan karin kudi euro 250,000 fiye da bara.

Talla

Monte Carlo Masters

Andy murray zai fara shirye shiryen shiga gasar French Open a yau Laraba inda zai kara da Edouard Roger-Vasselin a zagaye na biyu na gasar Monte Carlo Masters.
Rafeal Nadal kuma yana neman lashe kofin gasar Monte Carlo masters ne karo na 9 duk da dan wasan ya kwashe lokaci yana jinya.

Dan wasan Argentina Juan Martin Del Potro ya tsallake zuwa zagaye na biyu a Monte carlo bayan ya sha da kyar a hannun Alexandr na Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI