Kwallon Kafa

Madrid ta fi Manchester kudi, Backham ya fi Ronaldo da Messi

Beckham ya fi Messi da ronaldo samun kudi
Beckham ya fi Messi da ronaldo samun kudi topdrawer.com

A watan jiya ne Manchester United ta fafata da Real Madrid a gasar zakarun Turai, lamarin da ya ja hankalin masoya kwallon kafa a Duniya a karawar kungiyoyin biyu inda Real Madrid ta samu sa’ar United a Old Trafford. Kuma yanzu Real Madrid ta karbe wa United matsayinta na attajirar kungiya a jerin attajiran kungiyoyi kwallon kafa da Mujallar Forbes ke wallafawa.

Talla

Real Madrid ce ta daya a duniya da roron kudi Fam Biliyan biyu da Miliyan 18, Yayin da Manchester United ke bi mata da roron kudi fam Biliyan 2 da Miliyan 9.

Barcelona ce a matsayi na uku sai kungiyar Arsenal a matsayi na hudu, Bayern Munich kuma a matsayi na biyar.

Kungiyoyin Premier na Ingila Bakwai ne dai a jerin sahun attajiran kungiyoyin kwallon kafa 20, sai Bundesliga a Jamus da Seria A a Italia wadanda ke da yawan kungiyoyi Hudu. A Spain Barcelona ce da Real Madrid cikin jerin kungiyoyi 20 kamar yadda a Faransa akwai Lyon da Marseille. Kungiyar Corinthian daga Brazil ta samu shiga cikin jerin attajiran kungiyoyi 20. 

Jerin Attajiran kungiyoyin kwallon kafa a duniya

Dan Wasan PSG David Beckham shi ne na daya da aljihunsa ya fi cika da kudi Fam miliyan 33. Sai Ronaldo na Real Madrid a matsayi na biyu da kudi Fam Miliyan 28.8 abokin hammayarsa ne na Barcelona Lionel Messi a matsayi na uku da kudi Fam miliyan 26.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI