Kwallon Kafa

Roma ta doke Inter, Evian ta karya Lagon PSG

Dan wasan PSG, Zlatan Ibrahimovic
Dan wasan PSG, Zlatan Ibrahimovic REUTERS/Heino Kalis

A gasar Coppa Italia kungiyar Roma ta tsallake zuwa buga wasan karshe bayan doke Inter Milan ci 3-2 a San Siro. A cup de France kuma kungiyar Evian ta karye lagon PSG na fatar lashe kofuna biyu a bana bayan sun tashi wasa kunnen doki.

Talla

Zlatan Ibrahimovic da Thiago Silva ne suka barar wa PSG da Fanalty wanda hakan ne ya ba Evian nasara.

A League 1, PSG tana jagorarin teburin gasar ne da tazarar maki 9 kuma saura wasanni 6 a kammala wasannin, amma Evian tana matsayi na uku ne a saman kungiyoyi uku da ake wa barazanar ficewa gasar a bana

Yanzu dai Evian zata kara ne da Lorient, yayin da kuma Bordeaux da ta doke Lens ta fafata da Troyes a zagaeyn dab dana karshe a Cup de france da za’a gudanar da ranakun 7 da 8 na watan Mayu.
Jamus

A gasar cin kofin Jamus kungiyar Stuttgart ce yanzu za ta kara da Bayern Munich a wasan karshe bayan Stuttgart din ta doke Freiburg ci 2-1 a wasan kusa da na karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI