Premier League

Manchester United ta lashe kofin Premier karo na 20

Sir Alex Ferguson kocin Manchester yana murnar lashe kofin Premier karo na 20.
Sir Alex Ferguson kocin Manchester yana murnar lashe kofin Premier karo na 20. REUTERS/Phil Noble

Manchester United ta lashe kofin Premier karo na 20, bayan Robin Van Persie ya jefa kwalllaye uku a ragar Aston Villa a Old Trafford. United ta lashe kofin ne da tazarar maki 16 tsakaninta da Manchester City da ta lashe kofin a bara.

Talla

Wannan ne karo na 13 da Sir Alex Ferguson ke lashe kofin Premier. kuma yanzu kofuna 49 ke nan Ferguson yana lashewa tun fara aikin horar da ‘Yan wasa a Scotland da Ingila.

Farguson yace Van Persie ba ya da kwatance, Kuma a wasansu da Aston Vila ya zama gagari kowa.

A wasan Wayne Ronney ya yi haskawa karo na 400 a Manchester, Kuma dan wasan yace bana sun share hawayen bara da Manchester City ta lashe kofin.

Patrice Evra wanda a bara yace ba su taka kwallo ba kamar yadda suka saba da har ya ba Manchester City nasara. Amma dan wasan yace idan kana taka kwallo a United kuma baka lashe kofin Premier ba kamar baka kammala aikinka ba ne.

"Na yi imani da Manchester, idan ba ka lashe kofin league ba kamar ba ka kammala aikinka ba a matsayin dan wasan United” inji Evra.

Akwai wasu Muhimman wasanni da suka taimakawa United lashe kofin a bana. Kuma wasan farko shi ne wasan da Manchester ta doke Liverpool ci 2-1 a watan Satumba. Sai wasan da Manchester United ta doke Chelsea ci 3-2.

Manchester United tana neman kafa irin tarihin da Chelsea ta kafa na samun maki 95 idan har suka lashe sauran wasanninsu Hudu da suka rage, domin yanzu United tana da maki 84 a teburin Premier.

Sai a wasan karshe ne a ranar 12 ga watan Mayu za’a mikawa Red Devils kofinsu a Old Trafford.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI