Magoya bayan PSG sun yi arangama da ‘Yan sanda
Wallafawa ranar:
A Ranar Litinin an gudanar da bukukuwan lashe kofin League a Manchester da Barcelona da kuma Birnin Paris, sai dai ba wanye lafiya ba a bukin da PSG ta gudanar a Faransa domin an samu barkewar rikici da har ya yi sanadiyar arangama tsakanin magoya bayan kungiyar da ‘Yan sanda.
Wannan ne d karo na farko cikin shekaru 19 da PSG ta lashe kofin league din faransa mataki na farko,
A lokacin da kungiyar ke gudanar da bukin lashe kofin a birnin Paris ne kuma rikici ya barke tsakanin magoya bayan kungiyar da wasu ‘yan yawon bude ido.
An tabka hasara inda magoya bayan kungiyar suka abka wa gidajen shan barasa tare da farfasa gilashin gidajen cin abinci, lamarin da ya sa aka kwashe sa’o’I suna arangama da ‘yan sanda.
Yanzu dai mutane akalla 32 ne aka ruwaito sun jikkata, kuma rahotanni sun ce an cafke mutane 39 da ake zargin sun haifar da rikicin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu