Kwallon kafa

Jose Marinho ya koma Chelsea

Sabon Majan Chelsea Jose Marinho
Sabon Majan Chelsea Jose Marinho rfi

Sai mu shiga fagen manyan Club-club na kwallon kafa na Turai domin Jose Marinho n eke amsawa da bakinsa cewa shakka babu shakka babu ya koma Club din Chelsea.Ka san tun ajiya ne akayi ta yada cewa Jose Marinho, 50 ya sanya hannu cikin wata yarjejeniyar zama manaja a Chelsea.Tsohon Manajan Real Madris din zai kasance zagaye na biyu kenan yana yiwa Chelsea aiki, domin a shekara ta 2007 ya bar Chelsea sakamakon wata ‘yar takaddama da Attajiri mai Club din Dan Russia Roman Abramovich