Kwallon kafa

Japan ta yi nasarar zuwa gasar neman kofin kwallon kafa na duniya

Kan sarkin Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.
Kan sarkin Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.

Kasar Japan ta kasance kasa ta farko da ta samu nasarar zuwa gasar neman cin kofin kwallon kafa na duniya da za a gudanar a shekara ta 2014 a kasar Brazil, wannan kuwa bayan da ta doke Australiya a karawar da kasashen biyu suka yi a jiya talata a birnin Saitama na kasar ta Japan inda aka tashi wasa ci 1-1.

Talla

Japan dai ta samu wannan galaba ne rana ta 7 a ci gaba da karawar da ake yi domin fitar da kasashen da za su wakilci nahiyar Asiya zuwa wannan gasa, kuma wannan ne karo na 5 da Japan za ta samu halartar gasar neman kofin kwallon kafa na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI