Kofin Duniya

Czech da Italiya za su fafata a wasannin zuwa cin kofin duniya

'Yan wasan Italiya
'Yan wasan Italiya

A fagen wasannin fidda da gwanayen da za su halarci cin kofin duniya a Brazil a shekara mai zuwa, a yau ne, wato a rukunin Nahiyar Turai, Crotia za ta kara da Scotland, sannan Belgium ta karbi bakuncin Serbia a yayin da Czech za ta fafata da Italiya. 

Talla

Austria za ta kara ne da Sweden, kana Jamhuriyar Ireland ta fafata da Faroe Island.

Azerbaijan za ta gwada kaiminta ne da Luxemburg, kana Portugal ta karbi bakuncin Rasha.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI