Tennis

Jaridun Spain sun jinjinawa Nadal

Rafael Nadal yana murnar lashe kofin Roland-Garros karo na 8
Rafael Nadal yana murnar lashe kofin Roland-Garros karo na 8 Reuters

Bayan Rafael Nadal ya lashe kofin Rolland Garros karo na 8 inda ya doke takwaransa na Spain David Ferrer a wasan karshe. Jaridun Spain sun jinjinawa dan wasan a matsayin wani abin alfahari a kasar.

Talla

Nadal ya kwashe lokaci yana jinya amma yace kofin Rolland Garros kamar share fage ne ga wasu wasannin da ke tafe anan gaba.

“Sakamakon wasan yafi muhimmaci fiye da yadda muka fafata da David Amma wannan wani share fage ne a lokacin da na kwashe ina jinya” a cewar Rafael Nadal.

Yanzu haka dai Nadal ya shiga cikin kundin tarihin gasar French Open a matsayin mutum na farko da ya lashe kofin gasar karo na 8.

Labarin nasarar Nadal ne ya mamaye kanun labaran jaridun Spain musamman na wasanni.

Jaridar Daily Marca a birnin Madrid ta buga babban labarinta ne mai take “ Wani sabon farin ciki ga ‘Yan kasa” Jaridar tana mai cewa Nadal yanzu yana kafada da Roy Emerson da suka yi fice a duniyar Tennis.

Jaridar As Daily kuma a nata bangaren ta buga babban labarinta ne mai taken “Nadal ya karya tarihi”

Jaridar El Mundo Deportivo kuma a yankin Catalonia ta buga katon hoton Nadal ne a gaban shafinta mai dauke taken “ Rafa da kofuna 8”

Rafeal Nadal dai tun dawowarsa daga jinya a watan Fabrairu ya ke buga wasan karshe karo 9, inda kuma ya lashe kofuna 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.