Ingila

Mourinho yana cikin farin ciki bayan ya koma Chelsea

Sabon Kocin Chelsea Jose Mourinho a lokacin da ake gabatar da shi
Sabon Kocin Chelsea Jose Mourinho a lokacin da ake gabatar da shi REUTERS/Suzanne Plunkett

Jose Mourinho ya sauya suna daga “Special One” Na musamman zuwa sunan the “Happy one” wanda ke cikin farin ciki bayan kungiyar Chelsea ta gabatar da shi a matsayin sabon mai horar da ‘Yan wasan The Blues karo na biyu.

Talla

“Ina cikin farin ciki, domin wannan ne karon farko da na sake zuwa kungiyar da na ke so” inji mourinho

A baya dai Mourinho ya taimakawa Chelsea lashe kofin Premier sau biyu tsakanin 2004 zuwa 2007 kafin ya samu sabani da shugaban kungiyar, Attajirin Rasha Roman Abramovich. Kodayake Mourinho yace ya fice Chelsea ne cikin ruwan sanyi.

Mourinho dai ya yo kaura ne daga Spian zuwa Ingila bayan kammala kakar bana ba tare da ya lashe kofi ba a Real Madrid.

A daya bangaren, Rahotanni na cewa shugaban kungiyar Real Madrid Florentino Perez ya bayyana sha’awar daukar kocin PSG Carlo Ancelotti a matsayin mutum na farko da suke farauta wanda zai gaji Mourinho.

Sai dai kuma har yanzu kungiyar PSG ba ta ba Ancelotti damar shiga tattaunawa ba da Real Madrid wanda ya taimakawa kungiyar lashe kofin League din faransa karon farko tsawon shekaru da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.