Spain

Del Bosque yana lalaben dodon raga a Spain

Kocin Spain Vicente Del Bosque
Kocin Spain Vicente Del Bosque REUTERS/Ruben Sprich

Kocin Spain Vicente del Bosque yace har yanzu yana lalaben dan wasan da zai yi amfani da shi na din din a matsayin mai jefa kwallo a raga duk da ya yi amfani da Soldado da Juan Mata da suka taimakawa ma sa doke Jamhuriyar Ireland ci 2-0.

Talla

Del Bosque yana da zabin ‘Yan wasan da ke cin kwallon a raga da suka hada da Fernando Torres na Chelsea da kuma David Villa na Barcelona. Kodayake a gasar cin kofin Turai kocin ya yi amfani ne da Fabregas maimakon Torres.

A karshen makon nan ne Spain za ta fara kece raini da Uruguay a gasar cin kofin zakarun kasashen nahiyoyin duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI