Spain

Messi yana fuskantar badakalar haraji a Spain

Zakaran kwallon Duniya Lionel Messi sanye da rigar Argentina a lokacin da suke karawa da Colombia a Buenos Aires.
Zakaran kwallon Duniya Lionel Messi sanye da rigar Argentina a lokacin da suke karawa da Colombia a Buenos Aires. REUTERS/Marcos Brindicci

Masu gabatar da kara sun shigar da kara a Spain domin kalubalantar zakaran kwallon Duniya Lionel Messi akan wata badakalar haraji da aka yi zargin dan wasan ya yaudari ofishin haraji. Rahotanni sun ce adadin kudin badakalar sun kai sama da euro Miliyan 4, wanda ya shafi Messi da Mahaifinsa Horacio.

Talla

Amma kotun yankin Catalonia inda Messi ke zama ba ta bayar da izinin ci gaba da binciken ba, sai dai idan har aka gudanar da binciken lamarin zai zubar da mutuncin Messi da ake ganin yana da kima da mutunci fiye da sauran zaratan ‘Yan wasan duniya irinsu Cristiano Ronaldo.

Babu dai wani bayani daga kungiyar Barcelona amma Yanzu haka ana jiran Lauyan da ke kare Messi ya mayar da martan.

Zargin dai ya shafi harajin wasu hutunan Messi da ya ci kasuwa da su a kamfanin Adidas da Pepsi Cola da wani kamfanin abinci na kasar Kuwait daga shekarun 2006 zuwa 2009.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI