Kwallon kafa

An fitar da Togo zuwa gasar neman kofin kwallon kafa na duniya

Dan wasar Togo, Salifou Mustapha.
Dan wasar Togo, Salifou Mustapha. FP PHOTO/JUNIOR D.KANNAH

An fitar da kasar Togo daga sahun kasashen da ke neman zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a yi a shekara ta 2014 a kasar Brazil, bayan da ‘yan wasan Togo suka sha kashi a hannun takwarorinsu na Libya ci 2 da nema a karawar da suka yi jiya juma’a 14 ga watan Yuni.

Talla

Sakamakon wannan nasara da ta sama, a nan gaba Libya, za ta kara ne da Kamaru ko kuma Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo wadanda za su kara tsakaninsu domin fitar da zakara a ranar 17 ga wannan wata a birnin Kinshasa.
Mintuna 7 da soma karawa ne, ‘yan wasar Libya suka samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, kuma a lokacin ne Faisal Saleh ya zura kwallo a ragar kasar Togo.
Ana minti na 18 da soma wasar ne kuma mai bugawa kasar Togo Komlan Amewou, a kokarinsa na kare gidansu, ya sanya kwallon a cikin ragarsu a kan kuskure, lamarin da ya bai wa Libya galaba a kan Togo ci 2 da nema har zuwa karshen karawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.