Bundesliga

Dortmund ta jajajirce akan Lewandowski

Robert Lewandowski, Dan wasan Borussia Dortmund, wanda ya jefa kwallaye 4 a ragar Real Madrid a gasar zakarun Turai
Robert Lewandowski, Dan wasan Borussia Dortmund, wanda ya jefa kwallaye 4 a ragar Real Madrid a gasar zakarun Turai REUTERS/Phil Noble

Babban Jami’in Kungiyar Borussia Dortmund, Hans-Joachim Watzke ya shaidawa wata jaridar Jamus cewa babu inda dan wasan shi Robert Lewandowski zai tafi, duk da dan wasan ya kauracewa sabunta yarjejeniyar shi da kungiyar.

Talla

A kakar wasan da ya gabata, Lewandowski ya jefa wa Dortmund kwallaye 24 a raga.

Tuni dai Bayern Munich da ke hamayya da Dortmund a bundesliga ta yi ikirarin dan wasan ya amince ya kulla yarjejeniya da ita anan gaba.

Wannan ikirarin na Dortmund ya rufe kofa ga manyan kungiyoyin Ingila da ke farautar dan wasan irinsu Manchester United da Chelsea da kuma Manchester amma Dortmund ta karyata rahoton cewar ta linka wa dan wasan kudaden albashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.