Holland

An yanke wa Yaran da suka kashe alkalin wasa hukuncin dauri a Holland

Michael van Praag, shugaban kwallon matasan kasar Holland yana karrama  mataimakin alkalin wasan da aka kashe  Richard Nieuwenhuizen
Michael van Praag, shugaban kwallon matasan kasar Holland yana karrama mataimakin alkalin wasan da aka kashe Richard Nieuwenhuizen Reuters/Toussaint Kluiters/United Photos

Wata kotun kasar Netherlands ta yanke wa wasu Yara guda shida da mahaifin daya daga cikinsu hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari akan laifin tikawa wani mataimakin Alkalin wasa kashi da har ya yi sanadiyar mutuwar shi. Alkalin da ya yanke hukuncin yace Yaran sun yi wa alkalin mai suna Richard Nieuwenhuizen duka ne a kai da saman jikinsa, inda kuma nan take ne ya mutu bayan an kwashe shi zuwa asibiti.

Talla

Yaran sun fusata ne ga alkalancin mutumin da suka yi wa duka a wani wasan yara na ‘yan kasa da shekaru 17 a kasar Holland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI