Brazil-FIFA

Najeriya ta lallasa Tahiti a Brazil

Dan wasan Super Eagles Nnambi Oduamadi a lokacin da ya ke jefa kwallo a ragar Tahiti a Brazil
Dan wasan Super Eagles Nnambi Oduamadi a lokacin da ya ke jefa kwallo a ragar Tahiti a Brazil REUTERS

Dan wasan Super Eagles Nnamdi Oduamadi, shi ne ke da yawan kwallaye a gasar cin kofin zakarun nahiyoyin Duniya da ake gudanarwa a Brazil wanda ya jefewa Najeriya kwallaye uku a ragar Tahiti da aka tashi ci 6-1 a karawarsu ta farko.

Talla

Najeriya ce yanzu ke jagorancin rukuninsu na B inda ta karbe wa Spain matsayin da yawan kwallaye.

Wannan ne dai karon farko da Tahiti ta haska a wata babbar gasa amma duk da sun sha kashi be hanawa ‘Yan wasan murnar zira kwallo ba a ragar Najeriya domin kafa tarihi.

Najeriya dai ta barar da kwallaye domin Ahmed Musa da Anthony da Sunday Mba dukkaninsu sun yi gaba da gaba da raga amma suka barar da kwallayen.

Kocin Super Eagles na Najeriya Stephen Keshi yace ya godewa wa Allah da babu dan wasan shi da ya sake samun rauni saboda ‘Yan wasan shi hudu ya yi hasara da ke jinya, Victor Moses da Kalu Uche da Emmanuel Emenike da Ogenyi Onazi.

Akwai wasan kece raini tsakanin Brazil mai masaukin baki da kuma Mexico. Yayin da Italia da Japan zasu kara kuma Japan za ta yi kokarin fita kunya kada ta kasance kasa ta farko da ta kama hanyar ficewa gasar bayan tasha kashi a hannun Brazil a kararwar farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI