Faransa

Ribery da Benzama za su gurfana gaban kotun Paris

Franck Ribery Dan wasan Bayern Munich
Franck Ribery Dan wasan Bayern Munich REUTERS/Benoit Tessier

‘Yan wasan Faransa guda biyu Franck Ribery da Karim Benzema za su gurfana a gaban kotun Paris wadanda ake tuhuma sun yi amfani da wata karamar yarinya ‘yar asalin kasar Algeria da suka biya ta kudi. Idan har kotu ta kama su da laifi, ‘yan wasan suna iya fuskantar daurin shekaru uku a gidan yari tare da biyan kudaden tara euro dubu Arba’in da Biyar.