FIFA-Togo-Habasha

Togo da Habasha sun amsa laifin yin amfani da 'Yan wasan da ba su dace ba

Dan wasan Togo Salifou Mustapha.
Dan wasan Togo Salifou Mustapha. FP PHOTO/JUNIOR D.KANNAH

Kasar Togo ta bi sahun Habasha na amince wa da laifin sun yi amfani da dan wasan da be dace ya buga wasan neman shiga gasar cin kofin Duniya ba, Kakakin hukumar kwallon Togo shi ne ya amsa wannan laifin kamar yadda ya ke shaidawa manema labarai cewa sun yi amfani da dan wasan Kungiyar Marseille Alaixys Romao a wasansu da kasar Kamaru a ranar 8 ga watan Juni.

Talla

Dan wasan yana da katin gargadi ne guda biyu kuma ga ka’ida be kamata ya buga wasa na gaba ba.

Haka ma kasar Habsha ta amsa yin amfani da dan wasan da aka ba katin gargadi guda biyu a wasan da suka bi Botswana har gida suka doke ta ci 2-1.

Tun a makon jiya ne hukumar FIFA tace tana gudanar da bincike game da wannan matsalar ta yin amfani da ‘yan wasan da aka yi amfani da su masu katin gargadi.
Hakan dai zai sa nasarar da Togo ta samau ci 2-0, nasarar za ta koma akan Kamaru ci 3-0.

Kazalika, wannan ne zai budewa Afrika ta kudu kofa idan har aka hukunta Habasha.
Hukumar FIFA ta kaddamar da binciken akan Equatorial Guinea game da batun yin amfani da ‘yan wasan guda biyar da be kamata su wakilci kasar ba wadanda aka haifa a kasashen waje

A tsarin FIFA, duk dan wasan da ke son buga wa kasar shi ta gado wasa kuma wanda ba a Haifa kasar ba, to dole sai ya zauna a kasar akalla shekaru biyar .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.