Kwallon kafa

Gasar Zakarun Nahiyoyi: Brazil da Italiya sun wuce zuwa zagayen kusa da karshe, Najeriya za ta kara da Uraguay

'Yan wasan kasar Brazil a cikin farin ciki
'Yan wasan kasar Brazil a cikin farin ciki

A ci gaba da karawa a gasar cin kofin Zakarun Nahiyoyin Duniya a kasar Brazil, a daren da ya gababta an goga tsakanin kasashen da ke cikin gasar, inda kasar Brazil da kuma Italiya suka samu nasarar zuwa zagayen kusa da na karshe a wannan gasa, bayan da suka doke abokannin karawarsu. 

Talla

Ita dai kasar Brezil, ta samu nasara ne a karawar da ta yi da Mexico, inda aka tashi wasar ci biyu da nema a filin wasa na Forta-leza. Meymar ne dai ya soma zura kwallo a ragar kasar Mexico mintuna 9 da soma wasan, yayin da Jo ya zura kwallo ta biyu ana gaf da tashi wato ana mintuna 93 da soma wasan.

Ita kuwa Italiya ta sha dakyar ne a hannun kasar Japan a filin wasa na Racife, saboda an tashi ne ci 4 da 3 tsakanin kasashen inda Italiya ta yi nasarar ba zata. Kasar Japan ce ta soma sanya kwallo a ragar Italiya ana mintuna 21 da soma karawar, bayan da ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, kuma Keisuke Honda ne ya buga Penality.

An ci gaba da gudanar da wasar har zuwa mintuna na 33, inda Japan ta kara zura wata kwallo a ragar Italiya ta kafar Shinji Kagawa, lamarin ya sa tayar da kasar Italiya daga baci har ma ta samu nasarar zura kwallonta ta farko a ragar Japan ana mintuna na 41 tare da Daniele de Rossi, sai kwallo ta biyu Atsuto Uchida dan kasar Japan ya sanya wa ragarus a kan kuskure a mintuna na na 50.

Italiya ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida wanda Mario Balotelli ya zura kwallo a mintuna na 52 da soma wasan.

Japan ta sake farfadowa inda ta sake sanya kwallo ta uku a ragar Italiya mintuna na 69 (Shinji Okazaki ), amma ana mintuna na 86 da soma wasar, sai Sebastian Giovinco ya zura kwallo ta 4 a ragar Japan, lamarin da ya bai wa Italiya nasara.

To sakamakon wannan nasara dai, kowane daga cikin wadannan kasashe 2 da ke cikin Group A, na da maki 6, kuma wadannan kasashe ne za su kara da juna a ranar asabar mai zuwa idan Allah ya kai mu domin fitar da wanda zai je zagayen karashe na gasar.

To a can kuwa Group B, kasashen da ke ciki za su yi tasu karawar ne a yau domin fitar da wadanda za su kara a matsayin zagayen kusa da na karashe, da farko Spain da kuma Tsibirin Tahiti ne za su kece reni, sai kuma Najeriya wadda za ta kara da kasar Uraguay duk a yammacin yau.

To sai dai kamar yadda watakila aka sani, wannan gasa tana gudana ne a daidai lokacin da dubban mutane ke ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da yadda kasar Brezil ke kashe makuddan kudade wajen daukar nauyin wannan gasa da kuma wadda za a gudanar ta neman Kofin Duniya a shekara mai kamawa.
Shin wai meye jama’ar kasar ke adawa da shi a wannan batu? A ranar litinin da ta gabata, wato ranar farko ta wannan zanga zangar ta kece, akalla mutane dubu 250 ne suka mamaye titunan kasar, kuma hatta ma shahrarrun ‘yan kwallo a kasar ta Brezil kamar Dani Alves, da Hulk, da kuma David Luiz, sun ce ba su yi mamakin faruwar wannan tarzoma ba saboda wasu dalilai.
Da farko dai kasar ta kashe kudaden da yawansu ya kai Euro milyan dubu 11 domin daukar nauyin wannan gasa kawai, kuma wani abu da ya kara fusata jama’a, shi ne yadda sau da dama ana kara yawan kudaden da aka ce an ware domin gasar,
To su dai wadannan kudade, da dai za a rabawa mutanen kasar ta Brezil su milyan 194, da kowane mutum daya zai tashi da akalla Euro 57.
Har ila yau akwai batun rashawa da ya mamaye shirya wannan gasa ta Zakarun Duniya da kuma ta neman Kofin duniya da za a yi cikin sekara mai kamawa, saboda da dama daga cikin manyan jami’an tsara gasar cin kofin duniya na shekara mai kamawa cikinsu kuwa har da shugaban kwamitin tsare-tsare Ricardo Teixeira wanda tsohon dan kwallo ne, sun taba bayyana a gaban alkali dangane da wannan batu na rashawa, lamarin da ya kara harzuka jama’ar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI