Italiya-Brazil

Kocin Italiya ya nemi afuwar Balotelli saboda ya nuna masa wariya

Kocin Italiya Cesare Prandelli yana ba Mario Balotelli  darasi a gasar cin kofin zakarun Nahiyoyin duniya a Brazil
Kocin Italiya Cesare Prandelli yana ba Mario Balotelli darasi a gasar cin kofin zakarun Nahiyoyin duniya a Brazil REUTERS/Marcos Brindicci

Kocin ‘Yan wasan Italiya Cesare Prandelli ya nemi afuwar dan wasan shi Mario Balotelli saboda kalaman nuna wariyar launin fata da ya furtawa dan wasan a ziyarar da suka kai Brazil domin buga gasar cin kofin zakarun Nahiyoyin Duniya.

Talla

Saboda kaucewa zanga-zangar da ake yi a Brazil, kocin Italiya yace an kyale Balotelli ya fita daga masaukinsu a Salvadore don yana bakar fata.

Jardiar Daily Mail ta ruwaito kocin yana cewa Balotelli yana damar fita saboda fatar shi tana da banbanci da sauran ‘Yan wasa. Amma daga bisani Prandelli ya nemi afuwa yana mai cewa wasa ne ya ke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.