Tseren Keke

Ullrich ya amsa ya kwankwadi kwayu domin samun kuzari

Ullrich tare da Amstrong a gasar tseren keke
Ullrich tare da Amstrong a gasar tseren keke Robert Laberge/Getty Images

Tsohon zakaran gasar tseren keke ta Tour de France Jan Ullrich dan kasar Jamus ya amsa yin amfani da kwayu masu sa kuzari karkashin shawarar wani likitan kasar Spain inda a baya ya karyata yin haka.

Talla

Jan Ullrich wanda aka haramtawa shiga wasannin tseren keke na shekaru biyu a 2012 saboda ana zargin shi da kwankwadar kwayu masu sa kuzari, tuni ya amsa yana hulda da likitan tare da karyata ya taimaka masa.

Sai dai kuma a ranar Assabar, Ullrich ya shaidawa wata mujallar kasar Jamus cewa ya samu taimakon likitan mai suna Eufemiano Fuentes.

Ullrich yace yana da wahala a samu dan tseren keken da baya kwankwadar kwayu musamman a lokuttan baya.

Ullrich wanda ya yi ritaya daga tseren keke a 2007 bayan ya lashe zinari da azurfa a wasannin Olympics da aka gudanar a Sydney a 2000, shi ne dan wasan Jamus kacal da ya taba lashe gasar Tour de France.

Kwankwadar Kwayu ne dai yasa aka haramtawa Lance Armstrong kofunan da ya lashe guda Bakwai a gasar tour de France.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.