Liberia

Goerge Weah zai jagoranci wasan tawagar tsoffin ‘Yan wasan Afrika a Liberia

Tsoffin 'Yan wasan Afrika, JJ Okocha na Najeriya da Roger Milla na Kamaru da Goerge Weah na Liberia da Taribo West na Najeriya
Tsoffin 'Yan wasan Afrika, JJ Okocha na Najeriya da Roger Milla na Kamaru da Goerge Weah na Liberia da Taribo West na Najeriya ytttr.blogspot.com

Tsohon fitacce dan wasan Liberia George Weah zai jagoranci wani wasa na musamman da ya kunshi tsoffin zaratan ‘yan wasan Afrika domin tabbatar da zaman lafiya da sasantawa a kasar shi saboda yakin basasa da ya janyo hasarar rayukan mutane kimanin 250,000.

Talla

Goarge Weah wanda gwamnatin Liberia ta zabe shi a mastayin jekadan wanzar da zaman lafiya a kasar. ya gayyaci tawagar ‘yan wasa da suka hada da manyan tsoffin ‘yan wasan Kamaru guda biyu Roger Milla da Patrick Mboma, da JJ Okocha na Najeriya.

A ranar Assabar ne dai ake sa ran tsoffin ‘Yan wasan za su tara dimbin masoya a filin wasa da ke birnin Monrovia.

Goarge Weah ya taba lashe kyautar gwarzon dan wasan Turai a shekarar 1995.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI