Spain

Real Madrid ta tabbatar da Carlo Ancelotti a matsayin kocinta

Kocin PSG Carlo Ancelotti a lokacin da suke fafatawa da Barcelona a gasar zakarun Turai
Kocin PSG Carlo Ancelotti a lokacin da suke fafatawa da Barcelona a gasar zakarun Turai REUTERS/Gustau Nacarino

Kungiyar Real Madrid ta tabbatar da Carlo Ancelotti na PSG a matsayin sabon kocinta wanda zai gaji Jose Mourinho bayan ya koma Chelsea. Kungiyar Paris Saint-Germain kuma ta tabbatar da Laurent Blanc a matsayin sabon kocinta saboda ficewar Ancelotti. Tuni dai Shugaban Real Madrid Florentino Perez ya tabbatar wa wata Jaridar Spain cewa Carlo Ancelotti shi ne wanda zai gaji Mourinho.