Kwallon Kafa

Cristiano zai gana da Manchester akan makomar shi

Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo
Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo REUTERS/Juan Medina

A wani rahoto da wata jaridar Spain ta buga, jaridar El Pais, ta yi ikirarin Cristiano Ronaldo zai gana da Manchester United a cikin wannan makon game da makomar shi. Jaridar tace Ronaldo zai gana da wakilian Manchester kafin ya dawo hutu.

Talla

Wannnan labarin ya tabbatar da jita jitar da ake yi dan wasan yana shirin ficewa daga Real Madrid, kodayake dan wasan yace yana jin dadi a kungiyar illa matsalar shi da Florentino Perez.

A kwanakin baya an ta yada jita jitar Ronaldo ya kauracewa sabunta yarjejeniyar shi da Real Madrid, kamar yadda a ranar 13 ga watan Juni dan wasan ya yada a shafin shi na Twitter cewa jita jitar karya ne duk da bai fito ya yi karin bayani akan batun da ya ke karyatawa ba.

Tuni dai sabon kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana fatar Ronaldo zai bashi hadin kai, kamar yadda ya horar da Zidane da Ronaldo da Ronaldinho.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI