Tennis

Sharapova ta sha kashi a Wimbledon

Maria Sharapova a lokacin da ta sha kashi a gasar Wimbledon
Maria Sharapova a lokacin da ta sha kashi a gasar Wimbledon REUTERS/Stefan Wermuth

Maria Sharapova ta fice gasar Wimbledon a zagaye na biyu bayan ta sha kashi a hannun ‘yar wasan Portugal Michelle Larcher De Brito ci 6-3, 6-4. Wannan kuma na zuwa ne bayan Victoria Azarenka ta fice gasar da ake gudanarwa a Ingila saboda rauni, kuma ‘yar wasan ta fice ne dab da zata kara da Flavia Pennetta domin neman tsallakewa zagaye na uku.

Talla

Akwai kusan ‘Yan wasa guda hudu da suka fice saboda rauni, kuma sun hada daSteve Darcis wanda ya fitar Rafeal Nadal, da John Isner wanda ya doke Nicolas Mahut a shekarar 2010, a wata karawa da ba’a taba samun karawar da aka kwashe yawan lokaci ana fafatawa a tarihin Wimbledon bayan sun kwashe tsawon sa’o’i 11 da minti biyar suna fafatawa.

Yanzu haka dai filin wasan da ake fafatawa shi ne yanzu ya janyo muharawa bayan ficewar ‘yan wasa da dama saboda rauni. Victoria Azerenka, tace akwai bukatar a diba filin wasan domin ‘yan wasa suna darewa su fadi.

Daga cikin wadanda suka sha kashi kuma, akwai tsohuwar jarumar Tennis ta duniya Ana Ivanovic wacce ta sha kashi a hannun ‘Yar wasan kasar Canada.

Andy Murray ya tsallake zuwa zagaye na uku bayan ya doke dan wasan Taiwan Lu Yen-Hsun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI