Spain

Zidane ya zama mataimakin Ancelotti a Madrid

Zinedine Zidane Mataimakin mai horar da 'Yan wasan Real Madrid
Zinedine Zidane Mataimakin mai horar da 'Yan wasan Real Madrid

Real Madrid ta tabbatar da Zinedine Zidane da Paul Clement a matsayin wadanda za su taimakawa Carlo Ancelotti aikin horar da ‘Yan wasan kungiyar. Zinedine Zidane tsohon dan wasan Real Madrid wanda ya dade yana aiki karkashin shugabanci Florentino Perez

Talla

Sabon kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana farin cikinsa da damar day a samu na horar da ‘yan wasan kungiyar bayan ficewar Mourinho.

Sabon kocin wanda yayo sallama da Faransa a kungiyar PSG ya yi alkawalin kawo wa Real Madrid nasarori, sabanin kakar da ta gabata inda Madrid ta tashi a tutar babu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI