Wasanni

Brazil ta samu nasarar zuwa zagayen karshe

'yan kwallon kasar Brazil
'yan kwallon kasar Brazil

A ci gaba da gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa ta Zakarun Nahiyoyin Duniya, kuma a cikin daren jiya ne kasar Brazil ta samu nasarar zuwa zagayen karshe na wannan gasa bayan da ta doke kasar Uruguay ci 2-1 a filin wasa na Belo Horizonte.

Talla

Kasar ta Brezil dai ta samu nasarar zura kwallo ta farko a ragar Uruguay ana mintuna na 41 da soma wasar wanda Fred ya zura, to amma kafin nan kasar Uruguay ta samu gagarumar damar da za ta iya zura kwallo amma Allah bai yarda ba, sakamakon bugun daga kai sai mai tsaron gida da ta sama a minti na 15 da soma wasar, wanda Forlan ya shura amma mai tsaron gida na kasar Brazil Julio Cesar ya fitar da ita.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, kwallon ta dau zafi sosai a tsakanin bangarorin biyu, kuma minti uku kawai da dawowa, wato mintuna na 48 da soma wasa, sai Cavani na Uruguay ya zura kwallo a ragar Brazil, ya zama ci 1-1 kenan.

To haka dai aka ci gaba da wasa har zuwa minti na 86 lokacin da Brazil ta kara zuwa wata kwallo ta 2 a ragar Uruguay wadda Paulinho ya zura, abin da ke tabbatar da cewa Brazil ce za ta kara da daya daga cikin kasashen da za ta samu nasara a wasar da ake shirin bugawa a yammacin yau tsakanin Spain da kuma Italiya, kuma za a yi karawar ta karshe ne a ranar lahadi mai zuwa a filin wasa na Maracana da ke birnin Rio de Jenairo.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI