FIFA

FIFA ta datse wa Habasha maki uku

'Yan wasan Habasha suna karawa da 'Yan wasan Zambia
'Yan wasan Habasha suna karawa da 'Yan wasan Zambia Reuters/Thomas Mukoya

Kasar Afrika ta kudu ta samu karin kwarin gwiwa a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya a badi bayan an datse maki uku na kasar Habasha saboda ta yi amfani da dan wasan da be dace ba. Kasar Botswana ce dai yanzu hukumar FIFA ta ba nasara ci 3-0, bayan Botswana ce ta sha kashi a karawarsu da Habasha a watan jiya.

Talla

Kodayake an datse yawan makin Habsha amma har yanzu ita ke jagoranci rukuninsu da maki 10, yayin da Afrika ta kudu ke bi mata da maki 8, Botswana kuma a matsayi na uku da maki 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.